Falasdinawa 45,000 Ne Suka Yi Sallar Juma’a A Masallacin Al-Aksa A Birnin Kudus Da Ke Falasdinu

Mutane 45,000 ne suka yi gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa da ke birnin Qudus na Falasdinu Dubun dubatar matane ne suka gudanar da

Mutane 45,000 ne suka yi gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa da ke birnin Qudus na Falasdinu

Dubun dubatar matane ne suka gudanar da sallar Juma’a a masallacin Al-Aqsa mai albarka, duk kuwa da cikas da takunkumin da sojojin mamayar Isra’ila suka kawo na hana masallata isa masallacin.

Ma’aikatar kula da waqafin Musulunci a birnin Kudus da aka mamaye ta watsa rahoton cewa: Masallata 45,000 ne suka gudanar da sallar Juma’a a masallacin Al-Aqsa, da gudanar da sallar gha’ib wato sallar mamaci ga da baya nan domin tunawa da shahidan Zirin Gaza da yammacin gabar kogin Jordan.

Sojojin mamayar Isra’ila sun hana wasu samari da dama isa masallacin dake kofar tsohon birnin da kuma kewayen masallacin.

Sojojin sun tare matasan a kofar tsohon birnin, tare da duba takardunsu, sannan aka tilastawa wasu da dama daga cikin su ficewa daga birnin da kuma nisantar kusa da masallacin na Al-Aqsa.

Sheikh Muhammad Sarandah da ya gabatar da huduba a masallacin na Al-Aqsa a cikin hudubarsa ta Juma’a ya bayyana cewa: “Idan al’ummar Musulunci ta kamu da rashin lafiya ba za ta mutu ba, al’ummar Falasdinawa tana jinya amma ba ta mutu ba, al’umma ce dawwamammiya har zuwa ranar sakamako, tana ci gaba da raunana kuma ta yi rashin lafiya amma ba ta mutu ba.”

Ya kara da cewa, al’ummar musulmi an kokarin murkushe su a baya kuma a halin yanzu ma ana kan murkushe su, kuma ko da a ce al’ummar musulmi ta yi rauni da yunwa hakan ba zai sa a kawo karshen su ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted