Jagoran Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Abin da ake aikatawa a Gaza, laifi ne na karni
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya jaddada cewa: Irin wahalhalu da yunwa da ‘yan sahayoniyya suka haifar a Gaza abu ne mai muni, kuma laifi ne na karni. Ban da haka makiya sojojin mamayar Isra’ila na suci gaba da aikata laifuka iri-iri kan al’ummar Falasdinu a yammacin gabar kogin Jordan.
A cikin wani jawabi da ya gabatar dangane da ci gaban da ake samu na wuce gona da iri a zirin Gaza da kuma ci gaban yanki da na duniya, Sayyid Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya ce: Makiya yahudawan sahayoniyya sun aikata munanan laifuka a Gaza cikin wannan mako tare da jefa bama-bamai da kakaba yunwa. Ya yi nuni da cewa adadin shahidai a wannan mako sakamakon tashin bama-bamai da yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya ke yi ya kai dari, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai dubbai.