Uganda ta musanta amincewa da karbar ‘yan gudun hijira daga Amurka

Wani babban jami’in kasar Uganda ya musanta rahoton da kafar yada labaran Amurka ta fitar a ranar jiya Laraba cewa kasarsa ta amince da karbar

Wani babban jami’in kasar Uganda ya musanta rahoton da kafar yada labaran Amurka ta fitar a ranar jiya Laraba cewa kasarsa ta amince da karbar mutanen da aka kora daga Amurka, yana mai cewa “kasarsa ba ta da abubuwan da ake bukata don karbarsu.”

Tashar CBS News ta bayar da rahoton cewa, Washington ta cimma yarjejeniyar korar bakin haure da kasashen Uganda da Honduras, a wani bangare na kokarin da take yi na kara korar bakin haure zuwa wasu kasashen da ba kasashensu na asali ba.

Karamin ministan harkokin wajen kasar Uganda Okello Oryem ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, “A iyakacin  sanina, ba mu cimma irin wannan yarjejeniya ba,  Ba mu da kayan aiki da kuma kayayyakin more rayuwa da za mu iya daukar wadannan bakin haure a Uganda.”

Rahoton na CBS ya bayyana cewa, “yarjejeniyoyi tsakanin  Uganda da Honduras sun ta’allaka ne kan wani tanadi na dokar shige da fice ta Amurka, da ke ba da damar mika mutanen da ke neman mafaka zuwa kasashen uku bisa wasu sharudda na musamamn.”

Kasar Uganda dake gabashin nahiyar Afirka, wacce kuma ke kawance da Amurka, tana karbar ‘yan gudun hijira kusan miliyan biyu da masu neman mafaka, wadanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen yankin, irin su Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Sudan ta Kudu, da kuma jamhuriyar Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted