Majalisar Dinkin Duniya Ta Kara Gargadi Kan Mamayar ‘Yan Sahayoniyya A Zirin Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin ci gaba da fadada ayyukan sojojin mamayar Isra’ila a Gaza Falasdinawa 35 ne suka yi shahada tare da jikkatan

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin ci gaba da fadada ayyukan sojojin mamayar Isra’ila a Gaza

Falasdinawa 35 ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu da dama da suka hada da masu neman agajin jin kai guda 10 a ci gaba da luguden wuta da sojojin mamayar Isra’ila ke yi a yankuna daban-daban na zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Laraba. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da karuwar adadin wadanda suka yi shahada sakamakon yunwa, inda ta jaddada cewa, kimanin yara miliyan 1.2 na fuskantar barazanar yunwa.

Wuraren da aka takaita rarrabawa ya zama tarko na kashe mutane, kuma wadanda ba a kai musu hari ba, suna mutuwa saboda yunwa da rashin abinci mai gina jiki. Shahadan Falasdinawa da jikkata da suka hada da mace daya da wasu ‘yan mata biyu sun yi shahada tare da jikkata sakamakon harin bam da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan tarukan Falasdinawa a wurin rarraba kayan agaji a kudancin Wadi Gaza, baya ga wasu hare-haren da aka kai a tsakiyar zirin Gaza.

An kashe daukacin iyali da suka hada da wani mutum, matarsa, da ’ya’yansu uku, a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani tanti da ke dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke yammacin birnin Gaza. Wasu kuma sun rasa rayukansu tare da jikkata sakamakon harin da jiragen saman yakin suka kai a yankin Samer da ke tsakiyar birnin. Har ila yau jiragen yakin sojojin mamayar Isra’ila sun yi luguden wuta kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke arewacin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted