Kasashen Larabawa Da Kungiyoyinsu Sun Yiu Allah Wadai Da Shirin ‘Yan Shayoniyya Kan Gaza

Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Kasashe

Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza

Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan miliyan daya gudun hijira daga birnin Gaza da arewacin zirin Gaza zuwa kudancin kasar. A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Juma’a, sun yi la’akari da wannan shawarar da kuma shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a matsayin mai hatsarin gaske da zai haifar da bala’in jin kai a zirin Gaza kuma ba za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin ba, suna masu kira ga mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da wannan gurguwar tunaninsu maras kan gado.

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawan Tekun Pasha Jasim Muhammad Al-Badaiwi ya jaddada cewa; matakin da sojojin mamayar Isra’ila suka dauka na mamaye Zirin Gaza, yana wakiltar wani babban kalubale ga muradun kasashen duniya kuma lamari ne da ya saba wa dukkanin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, yana mai jaddada cewa, wannan mataki mai hatsarin gaske yana gurgunta duk wani yunkurin da ake yi na samar da zaman lafiya mai cike da adalci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted