Araqchi: Ba a kayyade lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, inda ya bayyana cewa, ba a kayyade lokacin shiga wasu shawarwari da Amurka ba, ya kuma tabo batun muhimmancin dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen Rasha, Sin da Masar.

A cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabijin na Iran , Araqchi ya jaddada bukatar samar da sabon tsarin hadin gwiwa tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, yana mai nuni da cewa, abubuwan da suka faru wanda ya kai  ga kaiwa kasar Iran hari bisa fakewa da rahotannin siyasa na  huumar IAEA, yasa dole ne Iran ta sake sabon salon a mu’amala ada wannan  hukuma.

Araghchi ya bayyana cewa, Tehran ta gayyaci mataimakin babban daraktan hukumar ta IAEA domin tattaunawa kan sabon tsarin dangantakarsu, yana mai jaddada cewa ziyarar ko alama ba za ta hada da duba cibiyoyin nukiliyar Iran ba, yana mai ishara da cewa Iran ba za ta mika kai bori ya hau ba.

Dangane da batun komawa kan teburin tattaunawa da Amurka  kuwa, Araghchi ya bayyana cewa, hakan ya dogara ne da muradu da maslaha ta kasar Iran, yana mai jaddada cewa, tattaunawar wani makami ne kawai na kiyaye muradun al’ummar Iran wajen mu’amala da Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted