Kungiyar Hamas Ta Wallafa Hotunan bidiyo Na Fursinan HKI tsare A Gaza

Ezzuddeen Qassam reshen soja na kungiyar Hamas a Gaza, ya wallafa hotunan bidiyo mai tsawon minti guda na daya daga cikin yahudawan Sahyoniya da take

Ezzuddeen Qassam reshen soja na kungiyar Hamas a Gaza, ya wallafa hotunan bidiyo mai tsawon minti guda na daya daga cikin yahudawan Sahyoniya da take tsare da shi a gaza, kuma a cikin hotunan kowa zai fahinci cewa bayahuden ya rame saboda rashin samin isashen abinci, ga kuma zafi a inda aka ajiyeshi a karkashin kasa.

Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya bayyana cewa, mutumin da qassam suka nuna a cikin hotunan shi ne Evyatar David, wanda Qassam ta kama tun ranar 7 ga wata octoban shekara ta 20230.

A ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 dai kungiyar Hamas ta kashe yahudawa 370 ta kama wasu 251. Bayan musayar Fursinonin a halinn yanzu kungiyar Hamas tana rike da yahudawa 49, daga cikinsu har da gawakin yahudawa 27 wadanda hare haren yahudawan a kan gaza ya halakasu.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted