Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu

Shugaban kasar Ivory Coast Alhassan Outtara ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na 4 wanda za a gudanar a watan Oktoba

Shugaban kasar Ivory Coast Alhassan Outtara ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na 4 wanda za a gudanar a watan Oktoba mai zuwa.

Za a yi manyan zabukan kasar ta Ivory Coast ne dai a ranar 25 ga watan na Oktoba mai zuwa.

Shi dai Alassan Outtara an sake zabarsa shugaban kasa karo na uku  a 2020, alhali tun a baya ya sanar da cewa zai sauka daga kan mukamin nashi.

Outtara ya zama shugaban kasar ta Ivory Coast a karon farko a 2010 a kasar da ita ce mafi girma wajen fitar da Coco a duniya.

Kamfanin dillancin labarun “Reuters’ ya amabto Ottata yana cewa: “Tsarin mulkin kasarmu ya ba ni damar in sake yin hidima a wani jikon, kuma inda da cikakkiyar lafiyar da za ta sa in yi hakan.”

Haka nan kuma ya ce; Ina sake tsaywa takara saboda kasarmu tana fuskantar kalubale mai girma a fagagen tattalin arziki da tsaro da ba a tsaba fuskantar irinsa ba a baya.

 Gabanin zamansa shugaban kasa, Outtara ya kasance kwararre a fagen tattalin arziki wanda ya yi karatunsa a kasar Amurka. Daga cikin ayyukan da ya yi da akwai gwamnan Bankin yammacin Afirka, sannan kuma mataimakin shugaban Asusun Bayar da Lamuni Na Duniya ( IMF).

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted