Iran Ta Jaddada Wajabcin Daukar Matakin Kawo Karshen Kisan Kare Dangi A Gaza

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza Mataimakin shugaban kasar Iran

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai na zahiri da kuma dauri daga kasashen duniya.

Aref ya rubuta a shafinsa na X a jiya Alhamis cewa: “Mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba saboda yunwa sakamakon hana isar da abinci ga al’ummar Gaza da aka zalunta ya kasance tare da yin shiru na kunya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.”

Ya kara da cewa: “Dole ne a kawo karshen wannan kisan kiyashi da ake yi a fili ta hanyar daukar matakai na zahiri da kasashen duniya zasu dauka, sannan kuma a hukunta wadanda suka aikata wannan laifin na cin zarafin bil’adama.”

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Zirin Gaza ta sanar a cikin wata sanarwa cewa: A cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kashe mutane 89 a zirin Gaza, yayin da wasu 453 suka jikkata.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted