A wani harin da sojojin mamaya Isra’ila suka kai ta sama sun kashe babban jami’in ‘yan sanda na Nuseirat da wasu mutane 11 na iyalansa
Babban daraktan ‘yan sanda a zirin Gaza ya sanar a jiya Asabar 19 ga watan Yulin shekara ta 2025 da shahadar Kanar Omar Sa’ed Aqel, daraktan ‘yan sandan yankin Nuseirat a yankin tsakiyar Gaza, sakamakon wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gidansa da ke garin Az-Zawayda a tsakiyar zirin Gaza.
Harin ta sama ya yi sanadin mutuwar mutane 11 na iyalan Aqel, wanda hakan ya nuna wani sabon kisan kiyashi da ya kara da cewa sojojin mamayar Isra’ila na cin zarafin jama’ar Falasdinu.
Hukumar ‘yan sanda ta jajanta wa Kanar Aqel, tana mai jaddada cewa, wannan laifi na daga cikin yakin kisan kiyashi da gwamnatin mamayar Isra’ila take yi wa al’ummar Falastinu sama da watanni 21. Ta kuma jaddada cewa, kai hari kan fararen hula da jami’an ‘yan sanda ba zai yi nasarar karya ra’ayin Falasdinawa ba ko kuma raunana kudurin jami’an ‘yan sanda, wadanda ke ci gaba da gudanar da ayyukansu na kasa da na jin kai na goyon bayan dagewar Falasdinawa ba.