Kasar Iran Ta Yi Gargadin Rugujewar Tsarin Shari’ar Duniya Saboda Son Rai Amurka Da ‘Yan Sahayoniyya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi gargadin rugujewar tsarin shari’ar duniya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi tsokaci kan murabus din

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi gargadin rugujewar tsarin shari’ar duniya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi tsokaci kan murabus din da mambobin kwamitin Majalisar Dinkin Duniya masu  bincike kan laifukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a Falasdinu, sakamakon matsin lamba da tursasawa da Amurka da gwamnatin ‘yan  sahayoniyya suke yi masa.

Baqa’i ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a yau Alhamis cewa: “Lokacin da wakilin musamman kan Falasdinu ya fuskanci cin zarafi da takunkumi, kuma mambobin kwamitin bincike kan yankunan da aka mamaye sun yi murabus gaba daya, hakan na nufin an daina barin cibiyoyin kasa da kasa su rubuta gaskiya.”

Ya ci gaba da cewa: “Murabus din da mambobin kwamitin binciken kan yankunan da aka mamaye, suka yi, biyo bayan sanya takunkumi kan wakilin na musamman, ba karamin lamari ba ne, lamari ne da ke nuni da rugujewar tsarin doka da ka’idoji na duniya.”

Ya yi nuni da cewa cibiyoyin kasa da kasa suna rasa halaccinsu, tasiri, iko da aikinsu, ya kuma ce: “Al’ummomi masu zuwa za su karanta cewa tsarin duniya ya ruguje ba saboda yaki ba, amma saboda shiru, rashin aiki, da nuna ma’auni biyu wajen fuskantar rashin adalci da zalunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted