Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta taimaka wajen hana bullar tashe-tashen hankula a yankin
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, wanda yake kasar China a matsayin shugaban tawagar hukuma domin halartar taron majalisar ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 25, ya gana da Wang Yi, sakataren kwamitin harkokin waje na jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar China, kana ministan harkokin wajen kasar ta China.
A yayin ganawar, ministocin harkokin wajen kasashen Iran da na Chjina sun yi nazari kan halin da ake ciki na shiyya da na kasa da kasa, inda suka tattauna tare da yin musayar ra’ayi kan muhimman batutuwan da suka shafi dangantakarsu.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yaba da yadda aka gudanar da babban taron majalisar ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 25, da nasarar gudanar da taron koli na majalisar ministocin kasar China, a matsayinsa na shugaban karba-karba na kungiyar, tare da yin kakkausar suka dangane da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da gwamnatin Amurka suka kai kan kasar Iran da take hakkin kasar Iran, da ketahurumin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa.
Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya tunatar da dangantakar da ke tsakanin manyan al’ummomin kasashen biyu wato Iran da kasar China a tarihi, ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na karfafa dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu da ya shafi dukkanin bangarori masu muhimmanci da suke gudana a kan tubhalin girmama juna da aminci.