Pir-hossein Kolivand, shugaban hukumar kwana-kwana ko kashe gobara na kasar Iran wato RED Cressen ya ce ma’aikatansa 5 ne suka rasa rayukansu a lokacinda suke aiki a cikin yakin kwanaki 12 da HKI a duk fadin Iran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Pirhossein Kolivand yana fadar haka a safiyar yau litinin a gaban yan jarida a ma’aikatan harkokin wajen kasar. Ya kuma kara da cewa HKI bata takaita hare-hare a kan fararen hula kadai a cikin yakin ba, sai dai bata bar ma’aikatan agaji kamar Hilal Ahmar ba.
Kuma kai hare hare kan ma’aikatan bada agaji, da kuma likitoci airin wannan halin ya sabawa yarjeniyar Geneva. Ya kara da cewa a hare-haren da yahudawan suka kai mashigar kurkukun Evin sun kashe jami’an gudanarwa da kuma shugabancin gidan yarin. Har’ila yau da asibitin da ke gidan yarin.
Daga karshe Pir-Hussain Kalivand ya bayyana cewa ya mika dukkan wadannan bayanan ga kungoyoyin kasa da kasa wadanda abinda ya shafa don su tabbatar da irin mummunan ayyukan da HKI ta aikata a cikin yakin kwanaki 12 da kasar Iran.