Jakadun kasashe 28 ne a nan Tehran suka kai ziyarar ginin ido ga ginin hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a jiya Lahadi, inda suka yi All..wadai da hakan suka kuma bayyana cewa wannan kokarin ruwa bakin yan jarida ne wadanda suke fadin gaskiya.
Kamfanin dillancin laraban IP na kasar Iran ya nakalto jami’an diblomasiyyar wadannan kasashen suna allawadai da HKI a yakin da ta dorawa JMI na kwanaki 12 ba tare da wani dalili ba. Sun kuma bayyana cewa yin haka ya sabawa dokokin kare yan jarida a lokacinda suke ayyukansu na yada gaskiya.
A ranar 16 ga watan Yuni ne makamai masu linzami na HKI da dama suka fada kan katafaren ginin na helkwatan na IRIB dake shiya na 3 a birnin Tehran ya kuma fada kan yan jarudu da kuma tashoshin talabijan da suke gudanar da shirye –shiryensu a na kai tsaye. Wanda ya jawo shahadar yan jarida guda uku da kuma kona ginin gabata.
Ginin wanda ake kira giransa ‘gidan gilashi’ yana dauke da ofishin shugaban hukumar gidajen talabijin da radiyo na kasar Iran wato IRIB, a hawa na 4 sannan akwai tashohin talabijin ta Khabar mai yada shirinsa kai tsare da harshen farisanci a duniya , inda a lokacin Sahar Imami take gudanar da shiti kai tsaye, sannan da kamfanin dillancin labaran Iran IRNA.
Sahar Imami a lokacinda take watsa labarai ta bada rahoto isar makami mai linzami na farko anna a lokacinda na biyon ya fada sai ya dauke wuta a dakin watsa labanran da take ciki. Tawgar jami’an diblomasiyyar dai sun hada da wasu kasashen Asiya, Afirka da kuma Laten Amurka.