Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa, tana nazarin sabuwar gayyatar da Amurka ta yi mana na komawa teburin tattaunawa.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto wata majiya mai karfi tana cewa, bayan da Amurka ta kasa dakatar da Shirin kasar na makamashin Nukiliya, ta aiko ma ta da takardar gayyata domin yin zama da ita akan teburin tattaunawa.
Majiyar ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fada wa kamfanin dillancin labrun “Mehr” cewa, Amurka ta aiko da sakwanni ta hanyar ‘yan aike na kasashe masu yawa.”
Ma’aikatar harkokin wajen ta Jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin nazari akan hakikanin abinda Amurkan take so, da kuma yadda tattaunawar za ta kasance wacce za ta zama ta dage takunkumai, da kuma darajar uranium din da Iran za ta tace, sannan kuma da biyanta diyyar barnar da aka yi mata sanadiyyar kallafaffen yaki.
Tun da dari, Amurka ta yi kokarin nuna cewa Iran ce ta bukaci ayi tatttaunawar, lamarin da Jamhuriyar musulunci ta Iran ta kore.
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Akarci, ya sha bayyana cewa, duk wata tattaunawa idan har za a yi ta, to za ta kasance ne akan manufar kare maslahar jamhuriyar musulunci ta Iran. Batun ci gaba da tace nadarin uranium kuwa, wani abu wanda Iran ba za ta taba ja da baya a kansa ba.