Kasar China Ta Yi Watsi da Barazanar Trump Na Kakabawa Kasashen BRICS Karin Takunkuman Tattalin Arziki

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta zargi kasar Amurka da nuna adawa da kungiyar BRICS ta raya tattalin arziki na kasashen kungiyar ta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta zargi kasar Amurka da nuna adawa da kungiyar BRICS ta raya tattalin arziki na kasashen kungiyar ta kuma kara da cewa kokarin kare kanta da ga shirye-shiryen BRICS ba zai amfane ta ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar China na cewa kungiyar kungiya ce wacce bata son babakere da Amurka take nunawa a yadda take tafiyar da al-amura a duniya kamar Ita ce, take iko da kowa.

Tace kungiyar tana son duniya ta zama mai kudubobi, wadanda su ma za’a iya fada su kuma aikata abinda suke so karkashin dokokin duniya. Don haka mamayar da takardan dalar Amurka ta yiwa mafi yawan harkokin kasuwanci a duniya bai yi masu ba. Sauran kasashen ma suna da kudade suna kuma son ganin sun fita daga danniya da babakeran da Amurka take ya a duniya.

Dole ne duniya ta zama mai kubobi, sai dai a yi aiki tare don tafiyar da al-amura a cikinta.

Kafin  haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump bayyana cewa zai kakabawa kasashen da suke cikin kungiyar BRICS takunkuman karin kodin fito na kasha 10% don kare kasar Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted