Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya

Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu Shugaban

Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba ne da za a iya rusa shi ta hanyar jefa masa bam saboda fasahar masana’antar nukiliya irin ta Iran tana bunkasa ce da ilimummukan masana ‘yan asalin kasa da suke da zurfin fasahar ilimin.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Mohammad Islami shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Laraba, don tattaunawa kan yadda gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka kai harin wuce gona da iri kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran, cewa: Wannan farmakin da aka kai kan Iran, wani rauni ne ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da kuma nuna cewa dokar daji ta mamaye duniya, kuma wadanda ba su da karfi ba za su iya ci gaba da rayuwarsu ba lamarin da tuni al’ummar Iran suka fahimci hakan da kyau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted