IPOB A Najeriya Ta Jawo Asarar Rayuka Kimani 700 Da Kuma Kudade Kimani Naira Triliyon N7.6 Tun Shekara ta 2021

Mutane kimani 776 ne suka rasa rayukansu sannan kudade kimani naira Triliyon N7.6 ne aka yi a sararsu a cikin shekaru 4 da suka gabata

Mutane kimani 776 ne suka rasa rayukansu sannan kudade kimani naira Triliyon N7.6 ne aka yi a sararsu a cikin shekaru 4 da suka gabata a yankin kudu maso gabacin Najeriya sanadiyyar zaman gida wanda kungiyar IPOB ta tilasta masu.

Jaridar Premium time ta Najeriya ta bayyana cewa rahoton hukumar tsaro na SBM Intelligence ta fitar a watan Mayon da ya gabata ya nuna cewa, da farko Kungiyar ta IPOB ta tilastawa mutanen yankin zama gida na don ganin an saki shugaban kungiyar Namdi Kano, amma daya baya sai ta zarce zuwa yanzu.

Kuma hakan ya hana abubuwan ci gaba da kuma harkokin kasuwanci makarantu da kuma ayyukan gwamnati tafiya.

IPOB dai tana bukatar warewa daga tarayyar Najeriya don kafa kasa mai suna Biafra daga yankin kudu da kuma kudu maso kudu na tarayyar Najeriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted