‘Yan Jarida Uku Sun Yi Shahada A Harin Da Sojojin Mamayar Isra’ila Suka Kai Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun kai harin wuce gona da iri kan yankin Gaza da ya yi sanadiyyar shahadan ‘yan jarida uku, sannan tsuna kai wani

Sojojin mamayar Isra’ila sun kai harin wuce gona da iri kan yankin Gaza da ya yi sanadiyyar shahadan ‘yan jarida uku, sannan tsuna kai wani harin bam kan asibitin Baptist a Gaza

Rahotonni sun sanar da kashe ‘yan jaridar Falasdinawa uku, yayin da wasu kuma suka jikkata a safiyar Alhamis, a wani sabon laifin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai musu, yayin da sojojin suka sake kai hari kan asibitin Al-Ahli Arab Baptist da ke birnin Gaza.

Majiyoyin kiwon lafiya a asibitin Baptist sun rawaito cewa wani jirgin mara matuki ciki na sojojin mamayar Isra’ila ya kai hari a harabar asibitin, inda ya kashe ‘yan jarida uku tare da raunata dimbin falasdinawa da suka fake a cikin harabar.

‘Yan jaridar biyun da aka kashe an bayyana sunayensu da ‘yan jaridar Falasdinu Today TV Suleiman Hajjaj da Ismail Badah, yayin da wakilin gidan talabijin na Al-Arabiya Islam Badr, da mai daukar hoto Ahmed Qaljah, da dan jarida Imad Dalloul suka samu raunuka daban-daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted