Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi.
A yayin wani jawabi da ta gabatar a wajen juyayin tunawa da rasuwar Imam Khumaini {r.a}, Pezeshkian ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta iya aikata wani aiki hauka da wauta ba, idan kasashen musulmi suka hada kansu.
Pezeshkian ya kara da cewa: Wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama suna kare “haramtacciyar kasar Isra’ila” mai laifi, kuma suna ci gaba da adawa da shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Ya ci gaba da cewa: “Babu mutum mai ‘yanci da zai yarda da zalunci da girman kai, kuma Iran ba zata yarda da shi ba.”
Pezeshkian ya bayyana cewa: “Za su dakile duk wani makirce-makircen abokan gaba kuma ba za su taba yin watsi da ‘yancinsu na nukiliya da na kimiyya ba.”