Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kuma kawayenta a wajen kungiyar wato (OPEC+) sun gudanar da taro a birnin Riyad na kasar Saudia a jiya Laraba, inda suka tattauna kan yawan man fetur da zasu haka daga shekara da ta 2027.
Shafin yada labarai na tanar gizo na kasar Saudia Arab News ya bayyana cewa wannan yana daga cikin abinda kasashe suka amince a bayan kuma a halin yanzu kungiyar ta rika ta tsara yawan man da ko wace kasa zata haka daga shekara ta 2022 har zuwa shekara ta 2026.
Labarin ya kara da cewa kungiyar tana da tsare tsaren haka man fetur har guda uku biyu suna tafiya kamar yadda suka tsara a yayinda daya kuma sun warewa kasashe 8 daga cikinsu su aiwatar da shi. Wannan tsarin yana daga cikin tsare tsaren kungiyar na dogon zango.
A halin yanzu dai farshin man yana kan $60 a cikin watan Afrilun da ya gabata, Sannan shi ne farashi mafi karanci tun shekaru 4 da suka gabata, kuma sana diyyar kara kudaden fiton da Trump yayi farashin ya tashi zuwa $65 kan ko wace ganga.