Ministan Harkokin Wajen Iran Yayi Tir Da Jakadan Burtaniya A Amurka Dangane Da Tashe Uranim A Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington,  Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington,  Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba barin Iran ta tashe makamashin Uranium a cikin kasar. Ministan ya kara da cewa Mandelson yana son ya karkatar da tattaunawan da Iran take da Amurka.

Ya kuma kara da  cewa Iran ce take sanar da kasashen turai yadda tattaunawa tsakanin Amurka da ita ke tafiya, tun Amurka ta waresu daga tattaunawar. Yace, idan har haka ne tunanin kasar Burtaniya wacce take cikin kasashen da suka sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu, yana ganin mai yuwa Iran ta dakatar da sanar da su abubuwan da ke tafiya a tattaunawar.

Ya zuwa zagaye har 5 wadanda Amurka da Iran suka tattaunawa dangane da shirin Nukliya na Iran dai, Iran ta nuna mata cewa hanata tace uranium a cikin gida, jan layi ne wanda ba zata amince da shi ba, kuma ya sabawa yarjeniyar NPT wacce ta bawa Iran wannan damar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted