Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Babban Abin Da Suke Bukata Shi Ne Daga Takunkumi

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin da suke bukata a duk wata tattaunawa shi ne a dage takunkumi Kakakin ma’aikatar harkokin

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin da suke bukata a duk wata tattaunawa shi ne a dage takunkumi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya jaddada cewa babban bukatar Iran a duk wata tattaunawa ita ce a dage takunkumin da aka kakaba mata ta hanyar da za ta kai ga samun sakamako mai ma’ana.

Isma’il Baqa’i ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau litinin cewa: A kwanakin baya ministan harkokin wajen kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, sannan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Italiya, a gefen shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka.

Ya kara da cewa: A gobe ne ministan harkokin wajen kasar Iran zai kai ziyarar aiki zuwa kasar China. Ya kuma kara da cewa, ana ci gaba da samun wasu ci gaba a daidai wadannan ziyarce-ziyarcen, yana mai jaddada cewa idan aka yi tambayoyi a kansu a yayin taron tambayoyi da amsa, zai ba da cikakkun bayanai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted