Tashar talbijin ta 12 ta bayyana cewa; Rusau din da hare-haren Hizbullah suke yi a cikin matsugunan da suke kan iyaka sun shafi gidaje 2.585, 1000 daga cikin gidajensu sun yi raga-raga.
Kafafen watsa labarun na HKI sun kuma ce kudin gyaran wadannan gidajen da Hizbullah ta rusa sun kai Shekal biliyan 5, wanda ya yi daidai da dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 300.
Kafar watsa labarun ta kuma ce; A cikin matsugunin Kiryat Shmona kadai da akwai gidaje 300 da su ka tagayyara, 64 daga cikinsu sun lalace sosai.
A cikin matsugunin Shlomi kuwa gidaje 360 ne su ka lalace.
Amma a cikin matsugunin Mudhalla kuwa gidaje 150 hare-haren na Hizbullah su ka lalata sosai, sai kuma wasu 250 da su ka lalace sama-sama.
A matsugunin Nahariya kuwa da akwai gidaje 190 da su ka lalace, daga cikinsu akwai 48 da sun tashi aiki.
A yau Alhamis ma dai harin na Hizbullah a garin Nahariya ya yi sanadiyyar halakar dan share wuri zauna daya, bayan da makami mai linzami ya fada akan gidan da yake ciki.