Kasar Lebanon ta sanar da adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin sa’o’i 24 da suka gabata
Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Mutane 59 ne suka yi shahada, yayin da wasu 182 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta watsa rahoton cewa: Mutane 59 ne suka yi shahida,yayin da wasu 182 suka samu raunuka, kuma adadin wadanda suka yi shahada tun bayan fara kai hare-haren yahudawan sahayoniyya kan kasar Lebanon a ranar 8 ga watan Oktoban shekara ta 2023 suka kai 3,445 da kuma jikkatan wasu 14,599 na daban.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta gudanar da ayyukan jarumtaka da dama na yau da kullum ta hanyar harba rokoki da jerin jiragen sama marasa matuka ciki da harba makamai masu linzami kan wurare masu muhimmanci kan haramtacciyar kasar Isra’ila domin nuna goyon baya da taimakon al’ummar Gaza da al’ummar Falastinu da kuma gwagwarmayar Falasdinawa.