Sakon ministar harkokin wajen Afrika ta Kudu na jajantawa al’ummar Gaza

Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu ta tunatar da al’ummar kasar game da gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata, ta kuma shaida wa mutanen

Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu ta tunatar da al’ummar kasar game da gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata, ta kuma shaida wa mutanen Gaza da su yi imani da ‘yanci.

A cewar jaridar Arabi 21, Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu Nalidi Pandour ta aike da wannan  sako ne ga al’ummar Palasdinu dangane da ci gaba da yakin kisan kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi a zirin Gaza.

A kwanakin baya Pandora ta jaddada a wani taro da aka shirya  kan batun  shari’a ta kasa da kasa domin gurfanar da Isra’ila kan kisan kare dangi a Gaza da kuma nuna goyon baya ga Palasdinawa, wanda aka shirya a birnin Landan fadar mulkin kasar Birtaniya, inda ta bayyana cewa, al’ummar Palasdinu su yi fatan samun ‘yanci, duk da cewa hanya ce mai matukar wahala, wadda ba za ta tabbata ba sai da gwagwaramaya.

Da take amsa tambaya game da sakonta ga mayakan Falasdinawa da suke gwagwarmaya da mamayar Isra’ila, ta ce: Ina so in gaya muku karshen maganar mahaifiyata. Mahaifiyata ta kasance tana cewa lokacin da muke gwagwarmayar neman ‘yanci, muna yin hakan ne da dukkanin rayuwarmu.

Da yawa daga cikin wadanda suka halarci taron sun tasirantu matuka da kalaman Ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu kan hakkin da Falastinawa suke da shi na yin gwagwarmaya domin neman ‘yancinsu da kuma fita daga karkashin leman zaluncin Isra’ila.

Idan dai ba a manta ba a cikin watan Disamban da ya gabata ne kasar Afirka ta Kudu ta shigar da kara kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa, duba da yadda take ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza., wanda ya saba wa yarjejeniyar yaki da aka rattaba hannu a kanta a Geneva kan haramcin Kisan kare dangi, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a shekarar 1948.

Bayan da Afirka ta kudu ta shigar da kara kan Isra’ila a gaban kotun duniya kan kisan kiyashin da take yi a Gaza, wasu  kasashe da dama da suka hada da Spain, Bolivia, Colombia, Mexico, Turkey, Chile da Libya sun shiga masu marawa  Afirka ta Kudu baya a kotun duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments