Yariman Saudiyya kuma Firayim Minista na Saudiya, Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya tabbatar wa Najeriya da goyon baya a cikin shirinta na gyaran tattalin arziki.
Jaridar Daily Nigeria ta bayar da rahoton cewa, Tabbacin ya fito ne lokacin da Yarima da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka gana a Riyadh a ranar Litinin a gefen taron koli na hadin gwiwar kasashen Larabawa da Musulmi.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun Bayo Onanuga, Mai ba da shawara na Musamman ga Shugaban kasa kan yada Labarai.
Shugabannin biyu sun tattauna wuraren hadin gwiwa, musamman a fannin mai da gas, aikin gona, kayayyakin more rayuwa, da kafa Majalisar Kasuwanci ta Saudi-Najeriya.
Najeriya na fatan kulla yarjejeniya da gwamnatin Saudiyya kan wata cibiyar cinikayya ta biyu da aka yi shirin samarwa mai darajar dala biliyan 5 tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin Saudiyya na Zuba Jari a Harkokin Noma da Dabbobi (SALIC) ya zuba jari na dala biliyan 1.24 a shekarar 2022 don sayen kaso 35.43% a kamfanin Olam Agri, daya daga cikin manyan kamfanonin noma na Najeriya.