Ayatullah Khamenei : Hizbullah ta juya daga wani karamin rukuni zuwa kungiya mai karfi

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce, “Hizbullah ta juya daga wani karamin rukuni na mayaka zuwa wata babbar kungiya mai

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce, “Hizbullah ta juya daga wani karamin rukuni na mayaka zuwa wata babbar kungiya mai karfi da za ta iya tilasta makiya … ja da baya.

Jagoran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da mambobin majalisar kwararru ta kasar yau Alhamis.

A karkashin jagoranci Sayyed Nasrallah, Hizbullah ta bada mamaki ta yadda makiya suke amfani da kayan yaki iri-iri da farfaganda, amma suka kasa, kuma da yardar Allah ba za su iya ba inji shi.

Ayatullah Khamenei ya yi watsi da jita-jitar da ake ta yadawa kan raunin da kungiyar Hizbullah ta samu bayan shahadar shugabanninta, inda ya kara da cewa har Hizbullah na da karfinta.

Ayatullah Khamenei ya mika gaisuwar ban girma ga Sayyid Hashem Safieddine da kuma shugabannin Hamas Ismail Haniyyah da Yahya Sinwar da kuma kwamandan sojojin Iran Abbas Nilforoushan wadanda Isra’ila ta kashe a watan Satumba da Oktoba.

Har ila yau Ayatullah Khamenei ya yabawa kungiyar Hamas, yana mai cewa ci gaba da yakin da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ke yi da Isra’ila na nuni da cewa an fatattaki gwamnatin kasar.

“Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi niyyar kawar da kungiyar Hamas amma ta kasa yin hakan bayan kisan kiyashin da ta yi wa mutane da dama.

Jagoran ya kara da cewa “Suna tunanin kashe shugabannin gwagwarmaya, zai kawo kasrehn kungiyar, amma sai ga shi Hamas na ci gaba da yaki da karfinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments