Joe Biden : Zan Mika Ragamar Mulki Cikin Tsari Da Lumana

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin mika ragamar mulki cikin tsari da lumana ga zababben shugaban kasar Donald Trump.  Biden ya kuma ce zai

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin mika ragamar mulki cikin tsari da lumana ga zababben shugaban kasar Donald Trump.

 Biden ya kuma ce zai rage dambarwar siyasa a kasar yayin wani jawabi da ya yi dazu a fadar White House, wanda shi ne na farko tun bayan nasarar da ‘yan Republican suka samu a zaben shugaban kasa da aka kada Kamala Harris.

Kafin hakan dama ‘yar takarar jam’iyyar ta democrat Kamala Harris ta amsa shan kayi hannun Donald Trump a zaben na ranar Talata.

Da take jawabi ga magoya bayan ta a birnin Washington, Ms Harris ta ce tane sane da alhinin da suke ciki, kuma ta sha alwashin bayar da goyon baya wajen mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin kwanciyar hankali.

Mataimakiyar shugaban kasar ta ce za ta ci gaba da yakin tabbatar da dimokuradiyyar Amurka, da kare doka da oda da kuma jajircewa wajen cimma nasarar abin da ta sanya a gaba.

A jawabi na farko da ta yi wa masoyanta bayan shan kayi a zaben, Ms Harris ta fara ne da sanar da su cewa tana sane da yadda suke ji a zukatan su, amma ta ce yanzu lokaci ne na aiki tare domin cimma nasarar mika mulki ga sabuwar gwamnati.

Share

3.5 2 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments