Macron ya yi kira da a baiwa Turai ‘yancin kai kan tsaro, Bayan Zaben Trump

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya nanata fatansa na ganin an karfafa dabarun cin gashin kai na nahiyar Turai bayan zaben Donald Trump. Macron ya

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya nanata fatansa na ganin an karfafa dabarun cin gashin kai na nahiyar Turai bayan zaben Donald Trump.

Macron ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron kungiyar hadakar siyasa ta Turai (EPC), a birnin Budapest.

kungiyar an kirkiro ta ne bisa shawarar Mr. Macron a watan Mayun 2022, ‘yan watanni bayan barkewar yakin Ukraine da Rasha.

Emmanuel Macron ya ce Donald Trump a matsayinsa na zababben shugaban kasar Amurka, zai dukufa wajen kare muradun jama’ar Amurka.

“Mutanen Amurka ne suka zabi Trump, kuma zai kare muradun Amurkawa, kuma abu ne mai kyau, Tambayar ita ce: Shin a shirye muke mu kare muradun Turawa?; Ina ganin wannan shine abun da ya kamata mu fifita,” inji shi.

Ba dole ba ne mu mika tsaron mu ga Amurkawa har abada,” in ji Macron.

Kasashen turai da dama dai sun shiga ruidani da fargaba game da makomar rikicin Ukraine a shugabancin Donald Trump.

Shugabannin Turai sun bukaci zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump da ya goyi bayan Ukraine da kuma kaucewa yakin kasuwanci da takwarorinsu na Turai.

Kusan shugabannin kasashen Turai 50 ne suka halarci taron kungiyar siyasa ta Turai a Budapest a daidai lokacin da ake ta samun takun tsaka tsakaninsu bayan da Trump ya samu nasara a zaben shugaban Amurka da aka gudanar a ranar Talata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments