Rahotanni daga Lebanon na cewa hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 53 a fadin kasar a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Hare-haren Isra’ila a cikin sa’o’i 24 da suka gabata sun kashe akalla mutane 53 tare da jikkata 161, in ji ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon.
Wannan ya kawo adadin wadanda sukayi shahada a hare-haren zuwa 3,103 da jikkata 13,856 tun daga watan Oktoban 2023.
A daya bangaren kuma Falasdinawa 78 ne sukayi shahada sannan an raunata wasu 214 a cikin sa’o’i 48 na baya bayan nan, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Hukumar kare hakkin farar hula ta Gaza ta ce mutane 12 ne aka kashe a halin yanzu a harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke yammacin birnin Gaza.
Akalla mutane shida ne sukayi shahada kuma a wani harin bam da Isra’ila ta kai a garin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda tashar talabijin ta Aljazeera ta rawaito.