Manistan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana dalilai 3 da suka sa aka yanke shawarar korarsa daga kan mukaminsa
Yoav Gallant, wanda fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kora daga kan mukaminsa na ministan tsaro, ya yi kira ga gwamnatin yahudawan sahayoniyya da ta yi kokarin dawo da fursunonin yahudawa da suke tsare a Zirin Gaza a raye, yana mai jaddada bukatar dukkan yahudawa a Isra’ila su yi aikin soja.
Gallant ya jaddada cewa: An yanke hukuncin sallamarsa ne sakamakon rashin jituwar da aka samu dangane da batutuwa guda 3, wanda na farko yana da alaka da batun daukar aiki, domin a ganinsa duk wanda ya kai shekarun shiga aikin soja, to dole ne ya shiga aikin soja.
Ya yi nuni da cewa sabani na biyu na da nasaba da dagewar da ya yi na dawo da fursunonin Isra’ila a Zirin Gaza cikin gaggawa, kuma wannan wata manufa ce da za a iya cimma ta da wani mataki na rangwame, wasu daga cikinsu na da zafi.
Ya ce sabani na uku na da nasaba da dagewar sa cewa dole ne a kafa wata hukuma da za ta bincika dalilin faruwar harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.