Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Firayi Ministan Pakistan a Islamabad

Ministan harkokin wajen Iran ya gana da firaministan Pakistan a Islamabad inda suka tattauna kan batutuwa da dama. Abbas Araghchi da Shehbaz Sharif  sun tattauna

Ministan harkokin wajen Iran ya gana da firaministan Pakistan a Islamabad inda suka tattauna kan batutuwa da dama.

Abbas Araghchi da Shehbaz Sharif  sun tattauna kan kokarin bunkasa alaka da kuma kawo karshen yakin kisan kiyashin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi a Gaza, da kuma wajabcin hana Isra’ila ci gaba da aikata irin wadanann ayyuka na ta’addanci.

Bayan isarasa birnin Islamabad, Araghchi ya shaidawa manema labarai cewa Iran da Pakistan suna da alaka ta musamman da ta samo asali daga makwabtaka da kuma alakar tarihi, cudanya tsakanin al’ummominsu, da kuma huldar siyasa, tattalin arziki, da al’adu.

Araghchi ya ce dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta kasance ta ‘yan uwantaka da abokantaka, yana mai cewa, a yayin wannan ziyara, za a yi kokarin yin nazari kan hanyoyin kara habbaka wannan alaka da kuma hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

A cewar sanarwar da gwamnatin Pakistan ta fitar, Sharif ya ba da fifiko kan kudurin kasar na karfafa alakar ‘yan uwantaka da Iran ta hanyar ci gaba da yin mu’amala mai kyau, da kuma inganta hadin gwiwa domin cin moriyar juna a dukkan bangarori.

Firaministan ya kuma jaddada goyon bayan da Pakistan ke baiwa al’ummar Palasdinu a fafutukarsu domin neman adalci  da’yancin kansu.

Ya yi kakkausar suka da kuma nuna matukar damuwarsa kan yadda Isra’ila ke ci gaba da gudanar da ayyukan kisan kare dangi ga al’ummar Palasdinu.

Firaministan ya kuma jaddada bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, da samar da hanyoyin isar da kayan jin kai ba tare da bata lokaci ba, da kuma bai wa al’ummar Palasdinu ‘yancin cin gashin kai, kamar yadda kudurorin MDD suka tabbatar musu da wannan hakki nasu.

Firaministan ya kuma nanata kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai kan Iran a ranar 26 ga watan Oktoba, yayin da yake jaddada goyon bayansa ga Iran da kuma tabbatar da ‘yancinta .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments