Shugaban Majalisar Gudanar Da Mulki A Sudan Ya jaddada Fatan Kawo Karshen Yaki A Kasarsa

Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan ya bayyana kwarin gwiwar kawo karshen yakin kasarsa tare da sake gina kasar Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki

Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan ya bayyana kwarin gwiwar kawo karshen yakin kasarsa tare da sake gina kasar

Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a gwamnatin rikon kwaryar kasar Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan, ya jaddada aniyar dagewar kasarsa, jama’a da sojoji, kan kare kasar Sudan da cibiyoyinta, da kuma jaddada aniyar Sudan na kalubalantar makirce-makircen da wadanda ya kira ‘yan tawaye suke kitsawa kan kasarsa, yana mai fatan ci gaba da wanzuwar Sudan kasa daya dunkulalliyar kasa tare da fatan kawo karshen yaki da kuma fara sake gina kasar.

Al-Burhan ya yi tir da abin da ya bayyana a matsayin cin zarafi da ‘yan ta’adda na Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suke aikatawa kan al’ummar Sudan, yana mai furuci da cewa; muggan laifukan da ‘yan tawayen Sudan suke aikatawa rusa kasa ce da kokarin shafe wayewarta da ababen more rayuwa.

Yakin Sudan dai ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 da raba jama’a da muhallinsu, inda a halin yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira sama da miliyan 11, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, yayin da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa suke ci gaba da yin kiraye-kirayen kawo karshen yakin da nufin ceto kasar ta Sudan daga bala’in jin kai da ya fara jefa miliyoyin mutane cikin yunwa da mace-mace sakamakon karancin abinci inda yakin ya kai jihohi 13 cikin 18 na kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments