Tsawa ta kashe masu ibada da dama a Uganda

‘Yan sandan Uganda sun sanar da cewa mutane 14 ne suka mutu sannan wasu 34 suka jikkata sakamakon wata tsawa da walkiya da ta fada

‘Yan sandan Uganda sun sanar da cewa mutane 14 ne suka mutu sannan wasu 34 suka jikkata sakamakon wata tsawa da walkiya da ta fada a kan wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewacin kasar, wadanda mazauna wurin ke halartar taron ibada.

Mai magana da yawun ‘yan sandan, Ketuma Rusuki ya ce: Har yanzu ba a tantance sunayen wadanda suka mutu ba, kuma hatsarin ya faru ne a wannan Asabar a yankin Lamu mai nisa.

Rosuki ya yi nuni da cewa, ba su samu wani rahoto kan tashin gobara a wurin ba bayan faruwar lamarin.

Mazauna sansanin Palabek, wanda galibi ya hada da ‘yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu, suna halartar taron ibada ne a wani gini da aka yin a majami’ar wucin gadi lokacin da tsawa ta fada a kan ginin da mutane a  ciki.

Saud a yawa dai ana samun guguwar isa mai tsanani da ruwan sama gami da tsawa da walkiya a wanann yanki da ke kasar Uganda da ke yankin gabashin nahiyar Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments