A wani rahoto na musamman da Cibiyar tattara bayanai ta Falasdinawa ta shirya, ta bayyana cewa a cikin watan Oktoba kadai ‘yan gwgawarmaya a yammacin kogin Jordan sun kai hare-hare akan sojojin mamaya har sau 445.
Hare-haren na ‘yan gwagwarmaya sun yi sanadiyyar kashe sojojin mamay 11 da kuma jikkata wasu 98.
Cibiyar tattara bayanai ta Falasdinawa ta kuma ce, ‘yan gwgawarmayar sun bude wuta har sau 47 akan ‘yan mamaya, sun kuma yi fada gaba da gaba da su har sau 37, 28 daga cikinsu ya kasance a yankin Jenin sai kuma 24 a Nablus.
A yankin na yammacin kogin Jordan da kuma birnin Kudus, Falasdinawa 46 ne su ka yi shahada a hannun sojojin sahayoniya da ‘yan share wuri zauna.
Bugu da kari a cikin watan na Oktoba ne wasu falasdinawa biyu masu sadaukar da kai, su ka kai hari a birnin Kudus wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan sahayoniya,’yan share wuri zauna 7 da kuma jikkata wasu 17.
Bugu da kari wani Bafalasdinen mai sadaukar da kai ya halaka wani dan share wuri zauna 1 da kuma jikkata wasu 9.