Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Nasara tana tare da gwagwarmayar al’umma
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi nuni da cewa: Gungun sharri da ke goyon bayan gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wanda hakan ke nuni da cewa bangaren gwagwarmaya yana fuskantar wannan gungun sharri, kuma da yardar Allah nasara tana ga bangaren ‘yan gwagwarmaya.
A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin da ya karbin bakwancin masu gudanar da bukukuwan tunawa da shahidan lardin Fars ta kudu maso yammacin kasar Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: A yau muna fuskantar wani babban lamari kuma mai muhimmanci da ke kafa tarihi kuma yana da alaka da yankin yammacin Asiya, Lebanon, Gaza da Gabar yammacin Kogin Jordan, lura da cewa kowane ɗayan daga cikin waɗannan abubuwan na iya zama tushen motsi na tarihi zuwa gare mu.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Idan ba don mutane irin su shahidi Yahya Al-Sinwar da suka yi yaki har zuwa karshen rayuwarsu ba, da makomar wannan yanki ya kasance wani abu na daban, .. kuma ba don manyan mutane kamar irin su shahidi Sayyid Hassan Nasrallah ba wanda ya hada jihadi da hikima da jajircewa da sadaukarwa ya kuma sanya su cikin fagen gwagwarmaya ba, da tarihin yunkurin gwagwarmaya ya kama wata hanya ta daban.
Jagoran ya yi nuni da cewa: Yahudawan sahayoniyya da masu goya musu baya na yammacin turai sun fuskanci gagarumin shan kashi, yana mai cewa: Wannan gwamnati ta ‘yan sahayoniyya ta gaza saboda a tunaninta za ta iya murkushe kungiyoyin gwagwarmaya cikin sauki, yana mai fayyace cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe fararen hula fiye da dubu hamsin wadanda ba su dauke da makamai, da kuma wasu fitattun mutane jagororin gwagwarmaya, sai dai wannan bai yi wani tasiri a fagen gwagwarmaya ba, inda har yanzu suke fuskantar gwagwarmaya da dukkan karfi da Azama, yana bayyana hakan a matsayin babban shan kashi ga yahudawan sahayoniyya.