Tinubu Ya Yi Watsi Da Bukatar Jingine Sabuwar Dokar Karin Haraji A Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye kudirinsa na kara haraji. Tun farko dai kungiyar

Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye kudirinsa na kara haraji.

Tun farko dai kungiyar Gwamnonin Arewa ce ta bayyana adawarta da kudirin tana mai cewa ya saba wa muradun jama’ar Arewacin kasar.

Haka ita ma yayin zaman da ta gudanar a ranar Alhamis, NEC ta ba shawarar jingine kudirin ƙara haraji domin buɗe ƙofar tuntuɓar dukkanin masu ruwa da tsaki.

Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a, Tinubu ya bukaci NEC da ta bari a aiwatar da sabuwar dokar harajin.

Sanarwar wadda ta yaba wa Majalisar Tattalin Arzikin dangane da shawarar da ta bayar, ta kuma tunatar da ita muhimmancin kara harajin domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Dangane da hakan ne Tinubu yake tunatar da duk masu bore a kan kudirin da ya riga da aike wa Majalisar Tarayya da cewa har yanzu kofar tuntube-tuntube ga masu ruwa a bude take.

Sanarwar ta ce shugaban ya ji duka koken da ake yi game da kudurin da bukatar janye shi da ake yi, to sai dai ya ce kudirin – wanda tuni aka fara muhawara a kansa a majalisar — ba za a janye shi ba, sai dai ya ce a iya yin wasu gyare-gyare a lokacin muhawarar majalisar da kuma jin ra’ayin jama’a.

Sanarwar ta kara da cewa “shugaban kasar bai aike da kudurin gaban majalisar ba, har sai da ya kafa kwamitin wanda kuma ya yi aiki na tsawon shekara guda yana tattara ra’ayoyi game da kudirin daga wajen masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki daga duka bangarorin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments