Tawagar Iran A Geneva Ta Jaddada Hakkin Kare Kasarta Daga Duk Wani Tsegeranci

Tawagar Iran a birnin Geneva ta jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen kare ‘yancin kasarta Tawagar Jamhuriyar

Tawagar Iran a birnin Geneva ta jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen kare ‘yancin kasarta

Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Geneva ta rubuta wa mambobin taron Majalisar Dinkin Duniya kan kawo karshen makamai nukiliya a duniya cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare ‘yancinta da kasarta ba, bisa tsarin dokokin kasa da kasa.

Tawagar ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta din din din a Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva, a wata takarda da ta gabatar wa mambobin taron neman kwance damarar makaman nukiliya a duniya ta bayyana jerin muggan ayyukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata da suka saba wa dokokin kasa da kasa da kuma wuce gona da iri kan kasar Iran da ‘yancin kasarta.

Tawagar ta Iran ta yi nuni da harin wuce gona da iri da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damasqas na kasar Siriya, da kisan gillar da ta yi wa shahidi Isma’il Haniyyah, shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas wanda ya kasance babban bako a Iran don halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar a Tehran, da kuma hare-haren da ta kai kan sansanonin soji da dama a cikin Iran, duk wadannan cin zarafi ne ga muhimman ka’idojin dokokin kasa da kasa, da keta kariyar da ofisoshin jakadancin suke da shi a yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da kudurorinta.

Ta kuma jaddada cewa: Iran tana da hakkin kare ‘yan kasarta da muradunta da tsaron kasarta kamar yadda doka ta 51 ta Majalisar Dinkin Duniya ta tanada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments