Sojojin Amurka Da Na Birtaniya Sun Kai Hare-Hare Kan Kasar Yemen

Rundunar sojin Yemen sun sanar da cewa: Sojojin Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare kan lardin Hodeidah na kasarta Majiyar rundunar sojin Yemen ta

Rundunar sojin Yemen sun sanar da cewa: Sojojin Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare kan lardin Hodeidah na kasarta

Majiyar rundunar sojin Yemen ta sanar da cewa: Sojojin Amurka da Birtaniya sun kaddamar da wani farmaki kan yankin lardin Hodeidah na kasar Yemen a yau alhamis.

Wata majiyar tsaro a lardin ta Hodeidah ta bayyana cewa: Sojojin Amurka da Birtaniya sun kaddamar da farmakin ne a kusa da jami’ar Hodeidah a gundumar Al-Hawk.

Kamar yadda majiyar tsaron Yemen ta bayyana cewa: A jiya Laraba ce sojojin Amurka da Birtaniya suka kaddamar da hare-hare ta sama a kan  filin jirgin sama lardin Hodeidah, kuma a ranar 18 ga watan Oktoba, sun kai farmaki sau biyu kan gundumar Ras Issa da ke Hodeidah. Sannan sun kai farmaki na uku ne a ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba a babban birnin kasar Sanaa, tare da kaddamar da wasu hare-hare kan yankin gabashin birnin Sa’ada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments