Babban Sakataren Hizbullah Ya Ce Fira Ministan Isra’ila Ya Tsira A Wannan Karo Amma Ya Saurari Gaba

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Fira ministan Isra’ila ya tsira a wannan karon, watakila lokacinsa bai zo ba tukuna a

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Fira ministan Isra’ila ya tsira a wannan karon, watakila lokacinsa bai zo ba tukuna a harin da ‘yan gwagwarmaya suka kai kan gidansa

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya gabatar da jawabinsa na farko bayan zabensa a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullahi wanda ya gaji shahidin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah, inda ya yi ishara da shirinsa na aiki a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullahi da tafarkin gwagwarmaya.

Sheikh Na’im Qassem ya bayyana cewa: Shirinsa shi ne ci gaba da gudanar da ayyukan shahidi Sayyid Hassan Nasrallah, yana mai jaddada cewa gwagwarmaya zata ci gaba da kasancewa a kan turbar yaki a karkashin tsare-tsaren siyasa da aka gindaya, yana mai cewa: Suna sane da matakan ci gaba da suke faruwa a wannan mataki.

Sheikh Qassim ya jaddada cewa: Goyon bayan Gaza ya zama wajibi domin fuskantar barazanar da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa daukacin yankin daga kofar Gaza, kuma al’ummar Gaza suna da hakkin kowa ya mara musu baya, don haka bai kamata a gabatar da wannan tambaya ga kungiyar Hizbullahi ba.

Sheikh Qassim ya yi nuni da cewa: A lokacin da aka fara yakin Gaza, fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce; Sun fara yakin ne saboda samar da sabon yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da daya daga cikin jami’an gwamnatinsa ya yi magana game da kafa matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a kasar Lebanon, kuma ministan tsaron ‘yan sahayoniyya Yoav Galant ya yi furuci da cewa: Fuskar Gabas ta Tsakiya zata canza daga Lebanon, Sheikh Na’im yana la’akari da cewa: Duk waɗannan bayanan sun nuna aniyar ‘yan sahayoniyya ne na kokarin aiwatar da bakar siyasarsu ta mamaya da murkushe al’ummar yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments