Watan Oktoba Ta Zame Bakin Wata Ga ‘Yan Sahayoniyya Saboda Mummunar Hasarar Rayuka

Wannan wata na Oktoba ya kasance bakin wata ga Isra’ila sakamakon halaka yahudawan sahayoniyya 80 yawancinsu sojoji da hafsoshi Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila

Wannan wata na Oktoba ya kasance bakin wata ga Isra’ila sakamakon halaka yahudawan sahayoniyya 80 yawancinsu sojoji da hafsoshi

Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana watan Oktoban shekara ta 2024 a matsayin “Bakar Oktoba” bayan sanar da mutuwar yahudawan sahayoniyya 80, mafi yawansu sojoji da jami’ai a yankin Zirin Gaza da kudancin Lebanon, baya ga dimbin ayyukan jarumtaka da ‘yan gwagwarmayar suka gudanar a yankin gabar yammacin kogin Jordan da aka mamaya.

Gidan rediyon sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya watsa rahoton cewa: An halaka yahudawan sahayoniyya 80 da suka hada da sojoji da ‘yan sanda 64 kuma a cikinsu 33 manyan jami’an soji ne a kudancin kasar Lebanon, sannan 19 a Zirin Gaza, da kuma wasu yahudawan sahayoniyya 16 da suka sheka lahira a wasu hare-hare daban-daban a cikin wannan watan, yahudawan saka bayyana shi a matsayin “Black Oktoba” Bakin Watan Oktoba.

Gidan rediyon ya bayyana cewa: An kashe jami’ai da sojojin gwamnatin Isra’ila 33 a wani yunkuri na neman kutsawa kudancin Lebanon ta kasa, da kuma 19 a hare-haren sojojin yahudawa da suke yaki ta kasa a Zirin Gaza a cikin wannan wata na Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments