Tawagar MDD A Lebanon Ta Fuskanci Hari Fiye Da Sau 30 A Watan Oktoba

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Labanon (UNIFIL) ta sanar da cewa fuskanci hare-hare da dama” tun farkon watan Oktoban nan mai shirin karewa. “Tun daga

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Labanon (UNIFIL) ta sanar da cewa fuskanci hare-hare da dama” tun farkon watan Oktoban nan mai shirin karewa.

“Tun daga ranar 1 ga Oktoba, UNIFIL ta lissafa fiye da hare-hare 30 da suka haifar da lalacewar kaddarorin Majalisar Dinkin Duniya ko kayan aiki ko jikkata sojojin kiyaye zaman lafiya,” in ji Andrea Tenenti yayin wani taron manema labarai na bidiyo.

 Akalla bakwai daga cikinsu da gangan ne,” in ji shi.

Ya kara da cewa “Abin da ya fi damun su shi ne lamarin da dakarun wanzar da zaman lafiya ke gudanar da aikinsu.

Kakakin ya nanata cewa, “A bayyane yake, ayyukan sojojin Isra’ila da na Hizbullah sun jefa dakarun wanzar da zaman lafiya cikin hadari.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments