Hamas ta mayar da martani kan sabbin shawarwarin tsagaita wuta

Sami Abu Zuhri mai magana da yawun kungiyar Hamas ya tabbatar da cewa, Hamas ta amsa bukatar masu shiga tsakani domin tattauna sabbin shawarwari game

Sami Abu Zuhri mai magana da yawun kungiyar Hamas ya tabbatar da cewa, Hamas ta amsa bukatar masu shiga tsakani domin tattauna sabbin shawarwari game da tsagaita bude wuta a zirin Gaza.

Ya kara da cewa tuni ake gudanar da tarurruka da dama kan wannan al’amari, tare da wasu shirye-shirye  bayan hakan.

A wani taron manema labarai, inda ya karanta wata sanarwa da kungiyar ta fitar, Abu Zuhri ya yi nuni da cewa, tawagar Hamas ta bayyana bude kofa ga duk wata yarjejeniya ko ra’ayoyin da za su rage wahalhalun da al’ummar Palastinu ke ciki a Gaza, da kuma tsagaita bude wuta, da za ta kai ga janye sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila  daga daukacin yankin, da bayar da tallafi, da kuma  cimma yarjejeniyar musayar fursunoni.

Da yake tabo halin da ake ciki a arewacin Gaza, jigon na Hamas ya jaddada cewa, mutanen yankin na fuskantar kisan kare dangi wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin wannan zamani, sama da makonni uku a jere.

Ya kara da cewa, hakan na zuwa ne yayin da Amurka da kasashen yammacin duniya ke ci gaba da goyon bayan Isra’ila, kuma a cikin wani yanayi na cin amana na Larabawa da Musulmi  da ya kai matakin gaza dakatar da kai hare-haren da kuma kai agajin abinci da magunguna, ko kuma karya shingen da yahudawa suka kafa wa.

Yayin da yake jinjinawa gwagwarmayar Palastinawa da dukkanin dakarun da ke adawa da zaluncin da ake yi musu a kasashen Lebanon, Yemen, Iraki, da dai sauransu, ya jaddada cewa: “Ba abin yarda ba ne ga shugabannin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma jam’iyyunsu su takaita kawai kalaman tofin Allah tsine ko Allahawadai da Isra’ila, wannan abin takaici ne a inji Abu Zuhri.

A cikin wannan yanayi, Abu Zuhri ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da na Musulunci da su sanar da wani kuduri mai cike da tarihi da ya dace da adalcin al’ummar Palastinu, da halastaccen hakkin al’ummar Palastinu, da girman sadaukarwarsu domin ‘yancin kasarsu da al’ummarsu da kuma kare wurare masu tsarki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments