Jakadan Turkiya A MDD Ya Nuna Kin Amincewa Da Harin HKI A kan Iran

Jakadan kasar Turkiya  wanda ya halarci zaman kwamitin tsaro na MDD ya yi suka akan harin da “ Isra’ila” ta kai wa Iran ya kara

Jakadan kasar Turkiya  wanda ya halarci zaman kwamitin tsaro na MDD ya yi suka akan harin da “ Isra’ila” ta kai wa Iran ya kara da cewa, manufar hakan shi ne samar da hayaniya da rikici a cikin yankin yammacin Asiya.

Jakadan na Turkiya a MDD Ahmad Yildiz  ya soki Isra’ila ne a yayin zaman musamman da kwamitin tsaro ya yi akan harin da Amurka ta kawo wa Iran.

A gefe daya ministan harkokin wajen Turkiya Halkan Fidan ya bayyana cewa; Ankara ba ta son duk wani rikici a cikin wannan yankin. Haka nan kuma ya kara da cewa, Idan har Iran ta kare kanta, to hakan hakkinta ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments