Mataimakin shugaban majalisar siyasa na kungiyar Hizbullah Alhaji Mahmud Qumadhi ya yi watsi da barazanar da “ Isra’ila” ta yi wa sabon sakataren kungiyar na kisa, yana mai kara da cewa: “ Barazanar Isra’ila ba ta firgita mu
Alhaji Muhammad Qumadhi ya kuma ce; Ko kadan wannan irin barazana ba ta cikin lissafi.
Ko kadan ba ma tsoron shahada, domin duk wani mukami da mutum zai karba a Hizbullah yana nufin cewa ya yanke zama shahidi, kuma sabon sakataren Hizbullah yana sane da hatsarin da yake zageye da shi, kuma ba ya tsoron barazanar Isra’ila.
Ministan yakin HKI Yoav Gallent ya bayyana cewa; Zaben Na’im Kassim da aka yi a matsayin sakataren kungiyar Hizbullah, ta wucin gadi ne’ da hakan yake nufin cewa za su yi masa kisan gilla.
Danagane da abinda ‘yan sahayoniyar su ka ambata na cewa sun rusa mafi yawancin makamai masu linzami na Hizbullah, mataimakin shugaban majalisar siyasar ta Hizbullah ya ce; Abinda ‘yan sahayoniyar su ka ambata karya ce tsagwaronta.
Sojojin sun riya cewa abinda kawai ya saura na makamai masu linzami na Hizbullah bai wuce kaso 20% , mataimakin shugaban majalisar shawara ya bayyana cewa: Har yanzu ba mu fara amfani da karfin da muke da shi na makamai masu linzami ba.