Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu, Hamas da Islamic Jihad sun taya Sheikh Naim Qassem murna a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar Hamas ta taya Sheikh Naim Qasem murna kan mukamin na babban sakataren kungiyar Hizbullah.
An bayyana cewa, nada Sheikh Naim Qassem a matsayin babban sakataren Hizbullah, zai farfado da kungiyar bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrallah.
Hamas ta kara da cewa: Muna kara jaddada matsayinmu ga sabon shugaban kungiyar Hizbullah, muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya taimake shi ya ci gaba da tafarkin jihadi da tsayin daka.
A nata bangaren kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinawa ta taya Sheikh Naim murna inda ta ce nadin lamari ne da ke nuni da irin karfin gwagwarmayar Musulunci ta Lebanon. »
A jiya Talata ne aka zabi mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qassem a matsayin sabon shugaban kungiyar inda zai gaji Sayyed Hassan Nasrallah wanda ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut a watan jiya.
Sheikh Qassem wani jigo ne a kungiyar Hizbullah, wanda ke rike mukamin mataimakin sakatare janar na kungiyar tun shekara ta 1991.
Ya halarci tarukan da suka kai ga kafa kungiyar Hizbullah a shekarar 1982.
Sheikh Qassem ya dade yana daya daga cikin manyan masu magana da yawun kungiyar Hizbullah.