Kungiyar Jihadul-Islami Ta Yaba Da Zaben Sheikh Na’im Qassim A Matsayin Sabon Babban Sakataren Kungiyar Hizbullahi

Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta bayyana zaben sabon babban sakataren kungiyar Hizbullahi da cewa lamari ne da ke tabbatar da jajurcewar ‘yan gwagwarmaya da karfin

Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta bayyana zaben sabon babban sakataren kungiyar Hizbullahi da cewa lamari ne da ke tabbatar da jajurcewar ‘yan gwagwarmaya da karfin tsayin dakansu

Kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Matsayin da Sheikh Na’im Qassem zaben Sheikh Na’im Qassim a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah a wannan mataki mai matukar muhimmanci, yana tabbatar da irin tsayin daka na gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon, da sake dawo da karfin yunkurinta da tabbatar da girman ikonta na fuskantar abokan gaba da rusa ta’addanci da kuma dakile shi.

A yau Talata 29 ga watan Oktoban shekara ta 2024 ne kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu ta gabatar da sakon taya murna da jinjinarta ga shugabanni da manyan jigogi na kungiyar Hizbullah da kuma sabon Jagoran kungiyar Sheikh Na’im Qassem wanda ya gaji Jagora shahidi Sayyid Hasan Nasrullahi da ya sadaukar da rayuwarsa a kan hanyar zuwa birnin Qudus domin kalubalantar girman kai na tsagerun yahudawan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments