‘Yan Sahayoniya Suna Yin  Furuci Da Cewa Sojojin HKI Suna Shan Kashi A Hannun ‘Yan Gwagwarmaya

Dan siyasar HKI mai tsattsauran ra’ayi Avigdor Lieberman ya bayyana cewa; sojojinsu suna shan kashi sosai a hannun ‘yan gwagwarmaya, domin ya zuwa yanzu sun

Dan siyasar HKI mai tsattsauran ra’ayi Avigdor Lieberman ya bayyana cewa; sojojinsu suna shan kashi sosai a hannun ‘yan gwagwarmaya, domin ya zuwa yanzu sun kashe musu sojoji 800, kuma wasu da adadinsu ya haura 11,000 sun jikkata.

 Shi ma shugaban kasar HKI Ishaq Herzog ya bayyana cewa harin ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata wani babban bugu ne da  kawancen gwgawarmaya su ka yi musu,kuma abinda wannan kawancen yake so shi ne shafe su baki daya.

Har ila yau, shugaban wannan haramtacciyar kasa, ya yi ishara da asara mai girma da tattalin arzikinsu ya fuskanta, wanda zai iya jawo yahudawa su fara ficewa daga “Isra’ila”.

Wata cibiyar mai rajin kare demokradiyya a Amurka ta bayyana cewa; Tare da cewa shekara daya ta gushe daga  kai harin 7 ga watan Oktoba, sai dai har yanzu HKI tana cikin makoki, sannan kuma tana cigaba da fuskantar asara mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments