Kasashen Ireland, Norway, Slovania da Sapain sun fitar da bayanin hadin gwiwa akan matakin da majalisar HKI ta “Knesset” ta dauka na haramta ayyukan hukumar agajin Falasdinawa ta ( UNRWA ).
Ma’aikatar harkokin wajen Ireland ta wallafa bayanin hadin gwaiwar a shafinta na Internet da a ciki ya kunshi cewa; hukumar ta “UNRWA” ta Majalisar Dinkin Duniya ce da take aiki a Falasdinu domin taimaka wa miliyoyin Falasdinawa ‘yan gudun hijira.
Bayanin ya cigaba da cewa, an kafa wannan hukumar ne domin ta rika tafiyar da rayuwar Falasdinawa ‘yan gudun hijira, da a wannan yanayin da ake ciki su ka fi bukatuwa da ita.
Kasashen 4 sun sha alwashin cigaba da bai wa Falasdinawa taimakon da suke bukatuwa da shi ta hanyar wannan hukumar,kuma sauran kasashen da wannan hukumar take da rassa a cikinsu, za su cigaba da bayar da taimakonsu.
A jiya Litinin ne dai majalisar HKI ta yi dokar hana duk wasu ayyuka da su ka shafi wannan hukumar ta ( UNRWA) a fadin Falasdinu dake karkashin mamaya.
Shekara daya bayan kirkirar HKI ne wato a 1949 MDD ta samar da “UNRWA” domin taimakawa Falasdinawan da aka kora daga garuruwansu da gidajensu. Ayyukanta kuma sun shafi koyarwa,kiwon lafiya a Gaza da kuwa yammacin kogin Jordan, haka nan a kasashen da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa suke.